Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne da maraicen ranar Litinin a wata hira ta musamman da muryar Amurka inda ya ce, gwamnatin sa ta bi duk matakan da suka dace wajen samarwa al’ummar Zamfara tsaro tare da aiki da dukan hukumomin tsaro a jiharsa amma hakarsu bata cimma ruwa ba lamarin da ya janyo gwamnatinsa ta fito da wannan sabbin dabarun kare al’umma.
A cewar gwamna Matawalle, shugaba Muhammadu Buhari ya bada duk ababen da jami’an tsaro ke bukata wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kawo karshen matsalolin staro a jihar Zamfara sai dai har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Matalle ya kara da cewa gwamnatinsa ta kaddamar da kwamitin aiwatar da aikin baiwa wadanda suka dace makamai doń karę al’umma inda membobin kwamitin suka hada da tsaffin kwamishinonin ‘yan sanda da manya-manyan tsaffin jami’an soji da sauran hukumomin tsaro don cimma nasara a aikin kawo karshen miyagun iri a jihar Zamfara.
Ku Duba Wannan Ma Motoci Kirar Cardillac 17 Muka Ba Sarakuna Ba 230 Ba - MatawalleHaka kuma, Matawalle ya jadada mahimmancin kafa rundunar tsaro ta musamman irin wanda aka yi a yankin arewa maso gabas kamar civilian JTF na Borno da na kudancin kasar tare da hadin gwiwar ‘yan Zamfara domin kawo karshen matsalolin tsaro a kasar yana mai cewa idan aka murkushe ‘yan ta'adda a Zamfara an sami nasarar kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya baki daya.
Gwamna Matawalle ya kara da jadada wa al’ummar jihar Zamfara cewa ko da jininsa na karshe a matsayinsa na wakilin al’ummarsa zai nema mu su sauki.
Haka zalika, Matawalle ya jinjinawa hukumomin tsaro ciki har da rundunar soji a jihar Zamfara kań aikin da suke yi, sai dai ya ce akwai karancin jami’ai kuma ana bukatar a turo kari.
A saurari bayani cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5