Dalilan Da Ke Sa Matan Yammacin Afirka Zuwa Turai Cirani

Bukin Festival Slam Na 'Yan Gudun Hijira A Jamhuriyar Nijar

Kungiyar matasan Plume du Sahel da hadin gwiwar reshen Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan cirani ( IOM ) sun shirya bikin Festival Slam a dandalin wasa na cibiyar raya al’adu da ake kira CCFN Jean Rouch da ke Yamai a Jamhuriyar Nijar.

An yi bikin ne domin bai wa mata ‘yan cirani damar fadawa jama’a matsalolin da suka tilasta masu barin gida, da irin wahalhalun da suka fuskanta a kokarinsu na zuwa turai ta barauniyar hanya.

Bukin Festival Slam Na 'Yan Gudun Hijira A Jamhuriyar Nijar

Galibin Matan da suka hau mambari a wannan wasa ‘yan asalin Afirka ta Yamma ne, cikinsu har da wata matashiya ‘yar Najeriya Faith Oche.

Oche ta ce, halin talaucin da ta tsinci kanta ciki sakamakon rasuwar mahaifanta, da tsufan da ya nakasa kakarta ne, ya ja ra’ayinta zuwa cirani.

Tashin hankalin da aka yi fama da shi a kasashe irinsu Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, shi ma ya yi sanadiyar ficewar ‘yan kasar da dama zuwa wasu kasashe makwabta.

Bukin Festival Slam Na 'Yan Gudun Hijira A Jamhuriyar Nijar

Wata ‘yar kasar Cameroun, Venerante Gongoye, da ta ratsa kasashen Chadi da Libya a kokarinta na zuwa kasar Jamus ta bayyana cewa sabanin da ya taso a tsakaninta da wasu kannanta maza ne, ya sa ta gudu daga gida.

Bikin wanda shi ne karo na farko da ake shirya makamancinsa a Nijar, an kuma karrama wadannan mata da lambobin yabo.

A saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilan Da Ke Sa Matan Yammacin Afirka Zuwa Turai Cirani