"Bayanda muka tsallake Katanga, mun rika jinmuryoyi na cewa mu dawo- mun yi tsammanijami’an ‘yan sanda ne, ashe ba mu sani ba, ‘yan bindiga ne. Daga nan su ka tara mu a wuri daya, a lokacin ne muka fahimci cewa, ‘yan bindiga ne sanye da kayan sojoji.” -- Usama Aminu
Wani yaro dalibin makaranta wanda ya kubuta daga hannun ‘yan tawayen Boko Haram masu da’awar jihadi ya yi bayani dangane da yadda aka sace su da kuma yadda ya kubuta.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin garkuwa da ‘yan makarantar 330 daga wata makaranta da ke arewacin Najeriya ranar jumma’a da ta gabata, a daya daga cikin hare hare mafi girma cikin shekarun nan.
Daya daga cikin ‘yan makarantar, Usama Aminu dan shekaru goma sha bakwai ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa sun girmi wadansu daga cikin wadanda suka tasa keyarsu.
Aminu yace “Mun kwana muna tafiya cikin jeji, da gari ya waye sai suka sami wuri suka ce mu zauna.”
Aminu, wanda ya ke fama da ciwon sikila ya koma makarantar ne kwanan nan domin ya yi kusa da gida inda za a rika kula da lafiyar shi.
Rundunar ‘yan sanda da mayakan sama sun kaddamar da farmakin hadin guiwa ranar asabar inda su ka yi musayar wuta da ‘yan bindigar bayanda suka gano inda maharan su ka boye a jejin Zango/Paula.
"Lokacin da ‘yan bindigar su ka ji karar jirgi mai saukar angulu yana shawagi sai su ka ce mana mu kwakkwanta karkashin itatuwa mu saukar da kawunanmu kasa,” in ji Aminu.
Aminu ya dafa kafadar biyu daga cikin abokan sa, “yayinda ‘yan bindigar su ka ci gaba da dukan daliban domin su sa su sauri.”
Duk da yanayin da ya ke ciki, ya yi kokari ya ja jiki a wani wuri da aka tsaya ya sami masallaci ya shiga ya boye.
Wadansu mutane a kauyen da suka ji shi yana tari suka bashi kaya ya sa ya cire unifom na makaranta domin badda kamannin shi.
Mahaifinsa ya ji dadin ganin dawowarsa ranar lahadi da yamma.
Aminu Ma'le ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, ya ji dadi da danshi ya dawo, ya kara da cewa, “ba zan yi murna domin dana ya dawo ba sabili da yara da dama har yanzu ba a san inda su ke ba.."
Tun farko gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce an ceto dalibai 17 da suka hada 15 da sojoji su ka ceto da kuma wani yaro guda da aka samu yana garari a jejin.
Ranar da aka kai hari, daruruwan dalibai sun tsere ta wajen tsallake Katanga lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin, ko kuma suka gudu lokacin da ake tafiya da su cikin jejin.
Kakakin shugaba Muhammadu Buhari Garba Shehu, ya ce gwamnati ta tattauna domin neman a sako su
Jihar Katsina ta rufe makarantun ta na kwana bayan da aka kai harin a makarantar sakandaren Kankara.
Gwamnatin jihar Zamfara da ke makwabciya da Katsina ita ma ta rufe makarantun kwana goma.
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, Kankara, da jihar Katsina.