Tara daga cikin daliban Allah ya yiwa rasuwa a hadarin yayin da sauran aka kaisu asibiti saboda a yi masu jinyar raunukan da suka samu.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya gana da iyayen yaran da 'yanuwansu a gidan gwamnati gabanin kawo gawarwakin daliban da maraicen jiya.
'Yanuwan wadanda suka rasa rayukansu sun fadi albarkacin bakinsu. Wasu sun yi addu'a Allah ya gafarta masu domin sun amince da duk abun da Allah ya yi.
Wata cikin kuka da juyayi tace mahaifin daya daga cikin yaran da suka rasu baya iya tashi saboda jikinsa sai gashi kuma ya rasa dansa.
Muhammad Dalhatu Adam da dansa yake cikin matattun yace Ubangiji ya fi kowa sani. Lokacin da suka samu labari abu ne mai sosa zuciya amma kuma babu abun da zasu ce saidai su yadda da abun da Allah ya yi.
Malam Ibrahim Khalil malamin addinin musulunci yace kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya fada duk wanda ya rasu a wajen bakunta ya yi mutuwar shahada. Saboda haka yaran da suka mutu a wajen bakunta sun yi mutuwar shahada. Irin wadannan abubuwa sukan faru domin Ubangiji ya nuna mana ikonsa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5