Daliban Da Aka Sako Sun Yi Zaman Jiran Ganin Shugaba Buhari a Katsina

Your browser doesn’t support HTML5

Daliban da aka sako sun yi zaman jiran ganin Shugaba Buhari.

Kusan mako guda bayan da wasu 'yan bindiga suka sacesu a makarantarsu ta kwana da ke garin Kankara a jihar Katsina, an kai daliban da aka sako su gaisa da shugaban Najeriya a Katsina.

Daliban makaranta maza fiye da 300, da aka sako bayan da aka sace su a makon da ya gabata a wani hari da aka kai a makarantarsu ranar Juma'ar da ta gabata, sun zauna a wani babban zaure suna jiran ganin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Jihar Katsina don ya gaisa da su ya kuma jajanta musu.

Daliban da aka sako.

Wani bidiyo ya nuna yaran barci na kwasarsu akan kujerun da suka zauna, babu shakka saboda wahalar da suka fuskanta a hannun wadanda suka yi garkuwa da su a ‘yan kwanakin da suka gabata.

A daren ranar Juma’a 11 ga watan Disamba ne aka sace daliban a makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke garin Kankara a jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.

‘Yan kungiyar Boko Haram masu da’awar jihadi a Najeriya sun dauki alhakin sace daliban. Madugun kungiyar Abubakar Shekau ya ce sun kai farmaki a makarantar ne saboda sun yi imani ilimin boko ya saba wa addinin musulunci.

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, Kankara, da jihar Katsina.