LAFIA, NAJERIYA - Lamarin ya auku ne a ranar Juma'a yayinda daliban suka kutsa wurin da gwamnatin jihar Nasarawa ta ajiye buhuhunan shinkafa da take niyyar rabawa daliban a matsayin tallafi.
Daraktan Hulda da Manema Labarai na gwamnan jihar Nasarawa, Ibrahim Addra ya shaida wa Muryar Amurka cewa sun sami labarin mutuwar mutane biyu, wassu fiye da ishirin suna kwance a asibiti ana musu jinya.
Bayanai da wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji, ta tattaro na nuni da cewa ba kadai dalibai ne suka shiga harabar da aka ajiye kayan tallafin ba, har ma da mutanen gari, saboda matsalar rayuwa da jama'a ke ciki.
Wani dalibi da aka yi turereniyar a idonsa, Mas'ud Usman yace tun cikin dare dalibai da mutanen gari, da adadinsu ya haura dubu shida suka yi cincirindo a gaban shingen wurin da aka ajiye kayan abincin.
Gwamnatin jihar ta Nasarawa dai ta umurci hukumomin jami'ar da na tsaro, su binciko yadda lamarin ya auku, da kuma zakulo wadanda ke da hannu a cikin lamarin don hukunta su.
Gwamnatin wacce ta jajantawa iyaye da jami'ar, ta kuma ce lamarin ba zai sa tayi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa daliban.
A saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5