A Najeriya, a daidai lokacin da daliban jami'o'i na kasar ke ci gaba da zaman gida suna shaukin ganin sun koma ajujuwan sa, sai ga wata hatsaniya ta barke wadda ta yi sanadin kara dakatar da wasu dalibai da yajin aikin malamai bai shafa ba.
Wannan ya faru ne a Sokoto inda dalibai suka kona wata daliba akan zargin yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) abin da ya sa aka rufe mkarantar har sai yadda hali ya yi kafin a kammala bincike.
Rikici tsakanin dalibai ba bakon abu ba ne a manyan makarantu da ke Najeriya abin da wani lokaci kan yi muni har a yi hasarar rayuka da dukiyoyi.
Irin hakan ne ya faru a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari wadda aka mayar Jami'ar Nazarin aikin malamanta ta jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda dalibai suka kona wata daliba akan zargin ta yi batanci ga fiyayyen halitta.
Wannan lamarin dai ya tayar da husuma tsakanin jami'an tsaro da aka turo makarantar domin taimakawa wadanda ke aiki wurin domin kwantar da husuma.
Binciken farko da jami'an tsaron da aka jibje wurin ya nuna yarinyar ‘yar asalin Rijau ta jihar Neja ce wadda ke karatu a sashen tsimi da tanadin gida “Home economics” ce abin ya rutsa da ita duk da yake ba su tabbatar da sakamakon binciken ba a hukumance.
Ma’aikatan tsaro dake makarantar sun yi kokarin kubutar da ita inda suka boye ta a ofishinsu dake cikin makarantar amma daliban suka balle ofishin suka kashe ta kuma suka cinna wuta da ita da ofishin duka suka kone.
A halin da ake ciki gwamnatin Sokoto ta maganta akan lamarin ta bakin kwamishinan yada labarai Isa Bajini Galadanci wanda ya tabbatar da lamarin ya kuma ce an akan gudanar da bincike.
Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta Sokoto ta fitar dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a, ASP Sanusi Abubakar, ta tabbatar da aukuwar tarzomar. Sanarwar ta kuma bayyana sunan dalibar a matsayin Deborah Samuel.
‘Yan sandan sun kuma ce an kama dalibai biyu da ake zargin na da hannu a lamarin yayin da tuni hukumomin jihar suka ba da umarnin a rufe makarantar tare da jibge jami'an tsaro.
Tuni dai jami'an tsaro na soji da ‘yan sanda da civil defence suka mamaye makarantar domin tabbabtar da doka a sassanta duk da yake an rufe ta lokacin da dalibai ke gudanar da jarrabawar kammala neman shaidar malanta.
Saurari rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5