Dakunan Jinya Dake Asibitin Suncika Makil Sandiyar Tashin Bom

People look at the wreckage of a car bomb outside the Education Ministry in Mogadishu, April 14, 2015. AFP PHOTO / MOHAMMED ABDIWAHAB

Cibiyar agajin gaggawa na asibitin kwararru dake Yola, a jihar Adamawa, ya kasance cikin rudani bayan wani harin bomb da aka kai a babban kasuwar Jimeta. wanda ya hallaka mutane da dama.

A lokacin da wakilin muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya ziyarci wurin ya samu mutane a kwance kan siminti sharba-sharba cikin jinni sakamakon raunuka da suka samu yayin da jami'an asibitin keta kai kawo na kokarin ceto rayukan su.

Mallam Sini wani dan kasuwa da wakilin muryar Amurka ya zanta da shi yace bomb din ya tashi a gaban shagon sa ne bayan da yaga samari biyu na cacar baki kafin tashin bomb din.

Mallam Saadu Bello na hukumar kai dauki na gaggawa na hukumar NEMA ya shaidawa muryar Amurka ta wayar tarho cewa gawarwaki 27 ne aka kwashe daga harabar.

Likitan Asibitin kwararru na Yola Dr Bala yace dakunan jinya dake asibitin suncika makil da jama'a wadanda harin ya rutsa dasu kuma suna bakin iya kokarin su wajen yi musu jinya.

Hakimin Jimeta Alhaji Baba Paris yace harin Bom din ba zata yazo lokacin da mutane suke dauka harin Boko haram ya lafa a jihar ta Adamawa.

‘’Wannan abu ya girgiza mu kwarai da gaske domin bamu taba tsammanin cewa irin wannan zai faru damu ba lokacin da ake tsananin wannan abubuwa.