Hukumar dakarun sojin saman Najeriya ta musa rahoton kashe fararen hula 16 a wani harin saman da jami’an ta suka auna ‘yan bindiga a yankin Tungar Kara a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Wani labarin da mujallar Zagazola Makama, mai wallafa labaran ta’addanci a yankin tabkin Chadi, ta wallafa a ranar Lahadi, ta ruwaito cewa wata majiyar leken asiri ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da ‘yan kungiyar sa kai na Zamfara Community Protection Guard (ZCPG), da mazauna al’ummar.
Sai dai a hirar shi da kafar labaran yanar gizo The Cable, darektan sashen hulhda da jamma’a na rundunar sojin saman Najeriya, Olusola Akinboyewa, ya musa zargin.
Akinboyewa y ace “Dakarun tsaron saman Najeriya suna takatsantsan wajen tabbatar da ragewa da kiyaye farma fararen hula a ayyukan da suke aiwatar wa.
“Akwai yiwuwar cewa ‘yan ta’addan da magoya bayan su ne suke yada rahoton a yunkurin karyata sojoji da farfaganda, duba da cewa suna shan kashi.”
Akinboyewa y ace babu sahihan rahotanni akan fararen hular da harin ya rutsa da su kuma an kai harin saman bisa sahihan bayanan sirri ne. Akinboyewa ya kara da cewa, “Duk da haka, ku tabata cewa dakarun sojin saman Najeriya tana dogaro da kwararan sahihan bayyanan sirri ne a yaki da ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da take yi daga majiyoyi mabanbanta sannan kuma a sake yin bincike don tabbatar da bayanan.