Dakarun Nijar Sun Tada Wata Maboyar 'Yan Ta'adda Intagarmay

Sojojin Nijar

An fara samun nasarar ayyukan tsaro na hadin gwiwa tsakanin kasashen Mali da Nijar masu fama da matsalar rashin tsaro.

Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijer ta yi nasarar kashe gomman ‘yan ta’adda a wata maboyar ‘yan ta’addan dake ikirarin jihadi a yankin arewacin Mali, lamarin da masana sha’anin tsaro suka bayyana da alama ce ta Zahiri dake fayyace tasirin aiyukan tsaro na hadin gwiwa a tsakanin kasashen da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga.

Samun izinin tsallaka makwabciyar kasar Nijar Mali domin fatttakar ‘yan ta’adda a duk lokacin da bukatar hakan ta taso na daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna akan su a yayin wani rangadin da babban hafsan hafsoshin Nijar Janar Salifou Mody yayi a farkon wannan wata mai ci na Maris shekara ta 2023 a birnin Bamako na kasar Mali.

Kayan aikin soji da gwamnatin Amurka ta ba Jamhuriyar Nijar gudummuwa

Ba da jimawaba bayan dawowarsa gida, sojojin kasa da na saman Nijar suka kutsa arewacin Mali inda suka rutsa ‘yan ta’addan a wani daji HAMAKAT da sahihan bayanan sirri suka tabbatar cewa nan ne maboyar ‘yan bindigar da suka kashe sojojin Nijar 17 a ranar 10 ga watan jiya a kauyen Intagarmay.

Sojojin sunyi nasarar hallaka ‘yan ta’adda saba’in da tara (79), sun kona Babura sama da dari (100) sannan a kwashe al’barusai masu yawan gaske da kuma na’urorin sadarwa a wannann farmakin da ya kasance na daukan fansa

Walikin Muryar Amurka, ya gana da wani mai sharhi a kan harkokin tsaro Moustapha Abdoulaye wanda ya yaba da yunkurin farfado da yarjejeniyar ‘yancin tsallaka iyaka a tsakanin Mali da Nijar.

Sojojin Kasar Nijar

Matakin ladabtarwar da kungiyar CEDEAO ta dauka kan Mali da Burkina Faso a sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen ya sa dangantaka tsakanin sojojin Mali da Burkina Faso da hukumomin makwabciyar kasa Nijar wace take karkashin mulkin domokradiya yayi tsami.

Domin uce takaicin matsin lambar da take fuskanta, gwamnatin rikon kwarya a Mali ta janye kasar daga cikin kungiyar G5 Sahel; matakin da ya maida hannun agogo baya a yaki da ta’addanci a yankin na Sahel. Nasarorin da askarawan Nijar suka samu sakamakon samun izinin bin sahun ‘yan ta’adda har cikin kasar Mali abu ne da ya kamata ya zama manuniya ga kasashen sahel a cewar masana.

Tun bayan wayewar garin ziyarar da Janar Salifou Modi ya kai Mali, masu bin diddigin al’amuran tsaro a kasashen Sahel irinsu Dr Seidik Abba suka ayyana abin a matsayin wani babban ci gaba a yunkurin neman hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro a wannan yanki.

Idan ba a manta ba, wani harin kwanton baunar da ‘yan ta’addan suka kai a kauyen Intagarmey kusa da garin TILOA na Jihar Tilabery a ranar 10 ga watna fabrairun wannan shekara ta 2023 ya yi sanadin kisan sojojin Nijar kimanin 17; sai dai rashin izinin tsallakawa cikin kasar Mali ya sa aka kasa daukar mataki akan maharan sakamakon rashin tsaro a bangaren Mali wanda shine ya kasance dalilin da ya sa babban kwamandan rundunar mayakan Nijer ya yi wannan rangadi da ya taimaka aka cire shinge a tsakanin kasashen biyu wadanda iyakar da ke tsakanin su ta kai tsawon sama da kilomita dari takwas (800).

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NASARORIN SOJAN NIJER A KASAR MALI (1).MP3