Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka wani kwamandan ‘yan ta’addan da ya yi kaurin suna, Munzur ya Audu tare da wasu mutanen 114 a jihar Yobe, ta hanyar jerin samamen da suka gudanar a fadin kasar.
Daraktan sashen yada labarai na ma’aikatar tsaron Najeriyar, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Ya kara da cewar dakarun na cigaba da kai hare-hare kan cibiyoyin safarar kayan bukatun ‘yan ta’addar da sauran gine-ginen da alaka da kungiyoyin ‘yan tada kayar bayan, inda ya jaddada cewar ana kokarin karya lago tare da wargaza dukkanin rassansu.
A cikin makon dake karewa, dakarun sun hallaka ‘yan ta’adda 115, tare da kama 238 da kuma kubutar da mutane 138 da aka yi garkuwa dasu.
A shiyar arewa maso gabashin najeriya kuma, dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na “operation hadin kai sun kashe ‘yan ta’adda 61, tare da kama 34 da kuma kubutar da mutane 32 da aka yi garkuwa dasu a cikin makon.