Dakarun Najeriya Sun Hallaka Dimbin ‘Yan Ta’adda A Zamfara    

A cewar sanarwar da jami’in dake, kula cibiyar yada labaran aikin wanzar da zaman lafiyar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, hakan ta faru ne da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Disambar da muke ciki,

Rundunar sojin Najeriya dake aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Fansar Yamma” tace dakarunta na hadin gwiwa sun yi nasarar gudanar da rangadin yaki a martanin da suka mayar ga wani kiran gaggawa da al’umma da ‘yan sintirin kauyen ‘Yar Galadima dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

A cewar sanarwar da jami’in dake, kula cibiyar yada labaran aikin wanzar da zaman lafiyar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, hakan ta faru ne da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Disambar da muke ciki, sa’ilin da aka ankarar da dakarun dake sansanin Hanutara dake jan ragama da misalin karfe 5 na asubahi cewar ‘yan ta’adda na kaiwa kauyen hari.

“Nan da nan dakarun suka maida martani ta hanyar kai dauki tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Yayin sintirin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addar da suka yi musu kwanton bauna a wurare 2 idan ana tunkarar kauyen.”

“Dakarun sun yi nasarar tarwatsa wuraren kwanton baunan tare da hallaka wasu ‘yan ta’addar sannan wasunsu suka arce. Sannan, nan da nan bangaren mayakan sama na aikin wanzar da zaman lafiyar “Fansar Yamma” ya tura jiragen sama domin kaiwa dakarun dauki ta sama yayin da suke tunkarar kauyen tare da yin musayar wuta da ‘yan ta’addar dake kokarin arcewa inda aka hallaka da dama daga cikinsu.”

Ya kara da cewar aikin wanzar da zaman lafiyar na Fansar Yamma ya dukufa wajen kawar da duk wata barazanar ‘yan ta’adda a shiyar arewa maso yammacin Najeriya da jihar Neja.