Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gowon Ya Bayyana Damuwa Da Karuwar Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya


Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon
Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon

Yayin da yake jawabi ga gamayyar ‘yan dimokiradiyyar arewa karkashin jagorancin Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, Gowon yace yana takaici game da matsalar rashin tsaron Najeriya.

Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Tsakanin 1966 da 1975, Yakubu Gowon, ya bayyana damuwa da karuwar matsalar tsaron dake addabar ‘yan Najeriya a bangarorin daban-daban na kasar, inda matsalar rashin tsaro ta kankama tsawon shekaru.

Yayin da yake jawabi ga gamayyar ‘yan dimokiradiyyar arewa karkashin jagorancin Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, Gowon yace yana takaici game da matsalar rashin tsaron Najeriya.

“Ina mai matukar takaici game da al’amuran dake faruwa a sassan kasar nan da dama, musamman a arewa. A ‘yan kwanakin nan nake samun labarin Lakurawa, wata kungiyar dake addabar al’ummar Zamfara. Na fahimci cewa sun tsallako ne daga kasar Mali. Wata sabuwar kungiya ta ketaro domin ta haddasa mana matsala,” a cewar Gowon.

Dattijon kasar ya kuma shawarci ‘yan arewa dasu zauna lafiya tare da warware matsalolinsu ckin lumana.

Lakurawa sun shiga jerin kungiyoyin ‘yan ta’addar dake salwantar da rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriyar dake zaune a yankin arewacin kasar.

Duk da cewa ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa mambobin kungiyar basu hauwar mutum 200 ba, wasu rahotanni na cewar kungiyar na yaduwa zuwa wasu sassan arewa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG