Dakarun Isra’ila Sun Yi wa Yankin Gaza Kawanya

Dakarun Isra'ila

Gungun ‘yan kasar waje na farko da suka makale a yankin Gaza tun bayan barkewar rikicin sun fara shiga Masar a ranar Laraba da wasu da yawa kuma a ranar Alhamis.

Dakarun Isra’ila na kafa sun yi wa yankin Zirin Gaza kawanya yayin da kasashen duniya ke kokarin ganin an tsayar da fadan da Isra’ila ke yi da mayakan Hamas a kuma daidai lokacin da jama’ar Gaza ke kara shiga tsananin kuncin rayuwa.

A ranar Laraba Shugaba Joe Biden ya nemi da a tsayar da fadan tsakanin Isra’ila da Hamas a mataki na jin-kai.

“Idan na ce a tsayar da fadan, ina nufin, samar da lokaci don fitar da a fursunoni.” In ji Biden.

Mayakan Hamas sun kama sama da Yahudawa 240 a ranar 7 ga watan Oktoba a wani hari da suka kai wa Isra’ila wanda ya halaka mutum 1,400.

Ba da bata lokaci ba Isra’ialn ta kaddamar da yaki akan Hamas tare da kai hare-hare a kai a kai, wadanda suka hlaka dubban Falasdinawa.

Ma’aikatar lafiyar Falasdinawa da ke karkashin ikon Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe sun haura dubu 9.

Gungun ‘yan kasar waje na farko da suka makale a yankin Gaza tun byan barkewar rikicin sun fara shiga Masar a ranar Laraba da wasu da yawa kuma a ranar Alhamis.