Dakarun tsaron Amurka suna fuskantar hare-hare da jirage mara matuka ko rokoki sau 27 a ‘yan kwanakin nan yayin da Amurkar take kara kai wasu dakarunta a yankin, a cewar Sakataren Tsaron Amurka, Loyd Austin a jiya Talata.
A kalla 7 daga cikin hare-haren sun auku ne bayan da dakarun Amurkar su ka yi sammakon kai wani hari wasu gine-gine a gabashin Syria inda mayakan Iran na Dogarawan Juyin Juya Hali da kawayensu ke amfani da.
Hare-haren Amurka din na zaman na ramuwar gayya bayan wasu hare-haren da aka kaiwa dakarunta sannan an tsara su ta yadda zasu kare tare da tsare jami’anta dake Iraqi da syriya a cewar sakataren tsaron Amurka Loyd Austin.
Babau daya cikin hare-haren gayyar na Amurkan da ya yi sanadiyyar kisar wani ko kuma barna a cewar jami’an tsaron kasar.
Harin baya-bayan nan shine wanda aka kai a jiya Litinin sannan tayi amfani da jirage mara matuka da ake kira one way drones domin kai hari filin sansannin dakarun sojin dake yammacin Iraqi da ake kira al –Asad bisa bayanan jami’an tsaron kasar da suka gana da wakilin Muryar Amurka inda suka bukaci a sakaya sunayen su.
Ryder, da sauran jami’an tsaro sun dora alhakin kai hare-haren da ake kaiwa dakarun na Amurka kusan a kowani wuni kan mayakan dake samun goyon byan Iran masu.
A jiya Lahadi, Austin ya shedawa ‘yan majalisar tarayyar kasar cewa, Amurka na da ‘yancin mai da martini a duk inda ta ga ya dace.