Dajin Sambisa Sunkuru ne Mai Wuyan Shiga

Wasu da aka kama a dajin Sambisa

A wata fira da wakilin Muryar Amurka yayi da wani dan majalisa ya bayyana yadda dajin Sambisa yake wanda ko a tsakar rana ba'a iya shiga cikinsa ba tare da fitila ba.
Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da wani dan majalisar tarayya da ya fito daga mazabar da ta kunshi dajin Sambisa a jihar Borno.

Peter Gumza mai wakiltar Gwozah da Damboa da Chibok a majalisar tarayya wanda kuma shi ne ya kasance yana wakiltar daliban da aka sace. Yace basu san halin da daliban ke ciki ba dalili ke nan shi da iyaye suna cikin wani mawuyacin hali. Ya kira wadanda suka sacesu muggayen mutane. Ba'a daukesu aure ba ba kuma makaranta suka je ba. An sacesu da nufin a cucesu a kuma ci zalinsu.

Peter Gumza ya dauki kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar asiri amma bata addini ba. Ba kungiya ba ce ta taimakawa jama'a, a'a, ta ta'adanci ce.An kafata ne domin a bata kasar Najeriya.Yace shin wane annabi ne yace a yanka mutane ana karbar jinisu. A nashi tunanin 'yan Boko Haram ba muslmai ba ne. Babu inda Kur'ani yace su sace 'yan mata, su kwashe kayan mutane, su kashe mutane babu wani dalili.

Mr Gumza yace 'yan Boko Haram su nemi wani suna na ta'adanci su sama kansu amma kada su hada kansu da wani addini. Dangane da cewa shi watakila bai san addinin Musulunci ba shi yasa yake ganin 'yan Boko Haram haka nan sai yace a gidansu shi kadai ne Kirista. Sauran Musulmai ne. Yace a cikin 'yanuwansa Musulmai an kashe wasu da yawa. Yace a halin da ake ciki an kashe Musulmai da Kiristoci da yawa. Yace an kashe hakimi kirista da hakimi muslmi. An kuma kashe kanwar sarkin garinsu musulma. Abun da kungiyar ke yi ba addinin Musulunci ba ne.

Gameda dajin Sambisa Mr Gumza yace yana cikin mazabarsa. Dajin nada fadin kilomita sittin ta kowane gefe. Yace idan an shiga dajin ba tare da tocilan ba to ko gaban mutum ba zai gani ba domin tsananin duhu. Dajin wani mugun sunkuru ne. Dajin nada bishiyoyi da namun daji iri-iri. Daga duka alamu hamada bata shiga kudancin Borno ba.

Ga rahoton Nasiru El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Dajin Sambisa Sukuru ne Mai Wuyan Shiga - 5' 24"