Dahiru Bauci Yayi Magana Kan Boko Haram

SHAIKH DAHIRU BAUCHI

Hare haren ta’addanci da tada boma bomai a guraren ibada, makarantu, kasuwanni da tashoshin mota harma da bankuna da gidajen mutane a arewacin Najeriya, alamune dake nuna gazawar gwamnatin kasa a bangaren tsaro, saboda haka ya zama dole al’umma su kare kansu domin gwamnati ta kasa samar musu da kariya, acewar Sheikh Dahiru Bauci.

Shahararren mai wa’azin musulinci a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana hakan awani taron manema labarai a gidansa dake Bauchi inda yace, “a matsayinmu ai mune ke fara cewa kowa yakare kansa tunda gwamnati bata iyawa,” yadai nuna cewa gwamnatin bazata iya kare mutane ba domin inda zata iya da ta riga tayi, ya kuma ce mutane su tabbatar sun kare kansu.

Sheik dai yace ‘yan Kungiyar Boko Haram sun nemeshi sukace suna son ya shiga tsakanin su da gwamnati a sulhunta, amma in har gwamnatin na neman sulhun, Sheikh dai yace insha Allahu duk abin da zai kawo zaman lafiya a Najeriya to yana ciki, sun dai fara taro a Bauci, shugaban kasa yace gwamnan Bauci ya wakilce shi kuma gwamnan Bauci yace duk da haka yana son ya aiko masa wani babban mutum daga fadar sa, sai ya turo masa Hassan Turkur an fara zama ana tattaunawa kamar da gaske.

Amma su kansu ‘yan Kungiyar Boko Haram din sun san cewa acikin gwamnati a kwai wadanda basa so ayi sulhun, saboda abu biyu na farko dai suna samun kudin da aka ware na tsaro kasa, na biyu kuma shine ana halakar da ‘yan arewa a haka dai maganar ta watse.

Tsokaci kan lamarin tabarbarewar tsaro a Najeriya daga bakin Shiekh Dahiru Bauci.

Your browser doesn’t support HTML5

Sheikh Dahiru Bauci - 3'48"