Rahotanni daga Jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu sun kai hari a wasu kauyuka uku na karamar hukumar Lau,dake jihar Taraba.
Bayanai sun yi nuni da cewa an samu asarar rayuka fiye da goma, baya ga kona gidaje da dukiyoyi da aka yi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan samun tashe-tashen hankula a tsakanin makiyaya da manoma a wasu jihohin Najeriya, batun da ke babbar barazana ga tsaron kasar.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wasu mahara da ake zargin ‘yan kabilar Bachama ne suka yi dirar mikiya a wasu kauyuka uku a wani yanayi mai kama da daukar fansa.
Sai dai kuma a martanin da shugabanin kungiyar al’ummar Bachama suka mai da, sun musanta zargin cewa su suka kai harin.
Mr. Euphraimu Paul Turaki, daya daga cikin shugabanin matasan Bachama, ya ce su ma an kai musu hari, to amma wannan ba su suka yi ba.
Kauyukan da aka kai wa harin sun hada da Bujum, Donada da kuma Katibu inda aka samu asarar rayuka baya ga kona gidaje.
Kuma cikin wadanda aka kashe har da Dagacin Katibu kamar yadda wani dan yankin ya tabbatarwa Muryar Amurka.
Mafindi Umaru Danburam shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihohin arewa maso gabas na daga cikin wadanda suka yi jana’izar gawarwakin ya kuma tabbatar da aukuwar harin.
Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohin biyu da a dau matakin gaggawa don hana kazancewar lamarin.
ASP David Misal, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Taraban, ya tabbatar da harin da kuma matakan da aka dauka inda ya ce tuni aka tura karin jami’an tsaro.
Saurari rahoton wakilinmu Ibrahim Abdulaziz domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5