Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Operation Lafiya Dole ta Kubutar da Mutane Fiye da 2000


Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole
Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole

Rundunar sojan Najeriya ta "Operation Lafiya Dole" dake aiki a shiyar Arewa-maso-gabashin Najeriya tace ta yi nasarar 'yanto mutane dubu biyu a yankin tabkin Chadi daga kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojan tace ta kubuto da wadannan mutane ne da suka hada da maza da mata da kuma kananan yara da yanzu haka take tantancesu. Har ila yau rundunar sojan ta kuma bayyana cewa ta samo daya daga cikin 'yan matan nan yan makarantar garin Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.

Yariyar da ta bada sananta Solomi Pagu ta kasance ta dari da bakwai da aka samu kwatowa daga cikin 'yan mata fiye da dari biyu da aka sace a cikin makarantar su ta garin Chibok. Sai dai rundunar sojan bata bada daman tattaunawa ba da yarinyar.

A makon da ya gabata ma, rundunar sojan ta Nigeria ta bada sanarwar 'yanto wasu mutane fiye da dari bakwai daga hannun ‘ya’yan kungiyar Boko Haram a arewacin jihar Borno. Wadannan nasarori da sojojin ke samu suna tabbatar da nasarar da suke ci gaba da samu a fafatikar da suke da mayakan Boko Haram.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG