Da safiyar yau Laraba wani bam ya tashi cikin wani masallacin dake garin Gamboru Ngala, garin dake kan iyaka da kasar Kamaru.
Tashin bam din ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara dake salla cikin masallacin tare da dan kunar bakin waken da ya sa adadin wadanda suka mutun ya kai goma.
Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da ake sallar asuba inda dan kunar bakin waken ya kutsa cikin masallacin dake anguwar Abuja. Na take ya tada bam dake cikinsa ya hallaka kansa da mutane taran dake salla a masallacin. Babu wanda ya tsira.
Wannan harin shi ne na farko da aka samu tun lokacin da mutane suka koma garin bayan an kwatoshi daga hannun 'yan Boko Haram da suka mamayeshi na wani dan lokaci.
Wani mazaunin garin ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan aukuwar lamarin. Ya tabbatar cewa harin cikin masallaci ya auku. Wanda ya kai harin shekarunsa zasu kai talatin da biyar. A cewarsa babu wanda ya jikata domin mutane taran dake salla a masallacin su ne suka mutu tare da dan kunar bakin waken. Harin ya rutsa da masallacin da mutane taran dake salla a ciki.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum