A cewar tsohon shugaban hukumar hadahadar kasuwanci ta Chambers of Commerce, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, an gina Najeriya ne da albarkatun noma.
“Najeriya da ta dogara ne da noma da sana’oin hannu, da kudin fata da na kirgi da na gyada da na auduga da na ridi da na cocoa hatta kudin da aka hako mai da kudin wadannan noma aka yi amfani.” In ji Dayyabu a wata hira da ya yi da Sasshen Hausa na Muryar Amurka.
A cewarsa yanzu ya rage ne ‘yan Najeriya su koma ga Allah su zabo shugabanni na gari domin a fitar da kitse daga wuta.
“Kuma Allah da ikonsa sai ya kawo wanda ya ke da zafin da kimar da kuma kokarin ya ga ya yi wadannan abubuwan, amma kuma shi ba dan siyasa ba ne kuma ya kasa tunanin yadda zai janyo ‘yan siyasa a jikinsa ta yadda za su rinka tunatar da shi kan abubuwa.” Ya kara da cewa.
Muryar Amurka ta kuma tambayi Alhaji Dayyabu, ko guguwar canjin da ta kada a Najeriay za ta samar da shugabannin na gari?
Domin jin amsar wannan tambaya, saurari karashen hirar da su ka yi da Grace Alheri Abdu:
Your browser doesn’t support HTML5