Tun bayan kin amincewa da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu bata dukiyar kasa ta EFCC, da shugaba Buhari, ya turawa majalisar har sau Biyu, ‘yan majalisar dattawan ke shan suka daga ‘yan Najeriya.
Dan kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Shehu Sale Rijau, ya ce bashi tare da abinda ‘yan majalisar dattawan suke yi, domin shugaban kasa keda hurumin kawo wanda yaga ya dace, dan haka shi ya ce yana bayan shugaba Buhari, domin ya tabbatar da yana yunkurin aiwatar da gaskiya ne.
Bisa dukkan alamu majalisar wakilai na shirin takawa majalisar dattijan burki biyo bayan kin tantance kwamishinonin hukumar zabe da shugaba Buhari ya turawa majalisar dattawan kamar yadda Shehu Sale Rijau, ya yi karin bayani.
Shugaban kwamitin labarai a majalisar dattawan Hon. Aliyu Sabe Abdullahi, ya ce surutan da ake yi akan su harma da zanga zangar nuna adawa da su duk ba wani bakon abu bane a siyasa, domin duk abinda za a yi sai wani ya ce bai yi masa ba dai-dai ba.
Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5