Farfasa Bube Na Maiwa yana fargabar kada Najeriya ta sake fadawa cikin irin halin da ta shiga a shekarar 1966.
Idan aka cigaba da tafiya haka wasu zasu yi kokarin ballewa. Misali jihohi ukun nan na arewa maso gabas wato Yobe Adamawa da Borno idan ba'a yi zabe cikinsu ba to suna iya su ce an waresu daga baya su hada hannu da 'yan ta'ada su kafa tasu daular. Komi na rayuwa ta yau da kullum ya tabarbare a jihohin.
Akan korafin da wasu 'yan Najeriya keyi na cewa gwamnatin shugaba Jonathan bata kudiri aniyar kawo karshen ta'adanci ba sai Farfasan yace lalle shi kansa yayi tunanen cewa gwamnatin kasar Najeriya na dari-dari da yakar ta'adanci. Akwai dalilin tunanen hakan domin har yanzu gwamnati bata yi anfani da kwararrun sojojinta ba wajen yakar 'yan ta'dan duk da taimakon leken asiri da take samu daga Amurka da Ingila.
Idan gwamnati tana son rikici ya cigaba shin wane riba zata samu. Farfasa Na Maiwa yace ribar da gwamnatin Jonathan zata samu ita ce rashin yin zabe. Yace kowa ya san gwamnatin Jonathan na fargaban zaben. Yana tsoron kada aka dashi a zabe sabili da haka idan rikici ya cigaba sai ya kafa dokar ta baci domin ya cigaba da mulki. Gwamnatin ta fito ta fadawa mutane gaskiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5