Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Kwace Sansanin Sojoji dake Baga


Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau.
Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau.

Bayan sun kwashe sa'o'i suna fafatawa, mayakan Boko Haram sun fatattaki sojojin Najeriya, Chadi, da Kamaru daga Baga.

A Najeriya mahara da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kwace wani sansanin soja a garin Baga dake jihar Barno.

Mazauna garin sun ce 'yan bindigar masu ikirarin musulunci sun fi karfin sojojin bayan da suka kwashe sa'o'i' suna bata kashi a sansanin da ke kusa da tafkin Cadi.

Rahotannin daga yankin sun ce sojoji da farar hula duk sun tsere bayan jerin hare hare da 'yan binidgan suka kai ranar Asabar.

Sansanin na hdin gwiwa ne inda ake yaki da miyagun mutane masu tsallaka kan iyakoki su shuka barna. Sojojin Nijar da Cadi, da Nijar su suke amfani da sansanin.

Ana zargin Boko Haram da kisan dubban mutane a cikin shekaru biyar yanzu da suka yi suna tada kayar baya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG