D’Tigress Ta Yi Nasara A Karon Farko Cikin Shekaru 20 Bayan Ta Lallasa Austireliya A Gasar Olympics

‘Yan matan Najeriya sun samu nasara a fafatawar da suka yi a yau Litinin a birnin Lille na kasar Faransa da ci 75 da 62.

Kungiyar kwallon kwando ta matan Najeriya (D’tigress) ta fara gasar Olympics ta bana dake gudana a birnin Paris da kafar dama, inda ta lallasa takwararta ta kasar Austireliya wacce ke mataki na 3 a duniya.

‘Yan matan Najeriya sun samu nasara a fafatawar da suka yi a yau Litinin a birnin Lille na kasar Faransa da ci 75 da 62.

Nasarar ta yau Litinin ita ce ta 2 ga Najeriya a wasan kwallon kwandon mata a gasar ta Olympics, inda ta farko ta kasance a 2004 lokacin da ta yi galaba a kan Koriya ta Kudu da ci 68 da 64.

Amma wannan shine nasarar D’Tigress ta farko a zagayen sharar fage data shiga har sau 9.

Wannan rashin nasara shine na 2 ga kasar Austireliya a wasan bude gasar kwallon kwando ta mata a wasannin Olympic. Gabanin wannan sun yi ikirarin samun nasara a wasanni 6 da suka yi a baya.

A yau Najeriya ta zamo kasar Afrika ta farko da ta yi galaba a kan Austireliya cikin wasanni 12 a gasar cin Kofin Duniya da ta Olympics.