A lokacin da asibitn ya sanarda kasar batun barkewar cutar mutane uku ne suka mutu saboda kamuwa da suka yi da kwayar cutar.
Bayan wani dan lokaci sai kuma adadin wadanda cutar ta kashe suka karu zuwa mutane bakwai. Yanzu kuma an sake samun karin mutane biyar. Adadin wadanda suka mutu a jihar sanadiyar kamu da kwayar cutar ya haura zuwa 12.
Shugaban sashen jinya na asibitin Dr. Atta Iliya yace yanzu ma akwai mutane 44 da ake zaton suna dauke da kwayar cutar. Akwai kuma wasu guda bakwai da suka tsere da ake zargin su ma suna dauke da kwayar cutar.
Da yake karin haske Dr. Inusa shugaban kiwon lafiya ta asibitin FMC yace sun dukufa wajen jinyar wadanda suka kamu da cutar zazzabin lassar. Ya kara da bayyana yadda ake kamuwa da zazzabin. Beraye ne ke dauke da kwayara cutar. Idan mutum ya yi anfani da abun da berayen suka yi fitsari ciki ko suka taba da bakinsu ana iya kamuwa da cutar. Idan kuma mutum ya yi muamala da wanda ya kamu da cutar shi ma yana iya kamuwa da ita.
Dr. Inusa ya ja kunnuwan mutanen karkara dake shanya tsari a fili kada su shanya inda beraye zasu yi fitsari a kai
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Taraba Dr Inusa Vaki ya bayyana irin matakan da gwamnati ke dauka. Yace gwamnatin jihar ta hanzarta ta bada magani domin kula da wadanda suka kamu. Ta kuma bada kudi a shiga karkara a fadakar da mutane akan cutar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5