Cutar Murar Tsuntsaye Ta Bulla a Maradi

Wata gonar kaji

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa an samu barkewar cutar murar tsuntsaye a wata gonar kaji da ke jihar Maradi.

Tabbacin barkewar cutar ya biyo bayan wani bincike da kwararru suka gudanar a kasar Italiya bayan da aka samu bullar cutar a gonar.

“Wannan murar tsintsaye tabbas ita ce aka samu bullar ta shekaran jiya a Kano.” In ji Darektan ma’aikatar kare lafiyar dabbobi a jihar ta Maradi, Salihou Isyakou.

Ya kara da cewa wannan nau’in cutar na iya kama mutane tana kuma musu illa yana mai jaddada cewa ya zuwa yanzu daga cikin kaji 4,140 da ke gonar saura 233.

“An kona kwai 29,000, da wasu 28,800 da ke cikin injin mai kyankyasa duk suma an fito da su an kona.” In ji Isyakou.

Bugu da kari Darektan ya kara da cewa an sa magunguna an feshe gonar a wani mataki na kare cutar fitar cutar daga gonar.

“Mun dauki jinin kaji a duk fadin gonakin da ke Maradi domin a je a gwada, hakan zai ba mu tabbacin ko cutar ta yadu ko bata yadu ba.

Yanzu haka masu kiyon kaji sun fara nuna korafin cewa wannan harka ita kadai suka sani kuma ba su da wani abin yi sai ita.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Murar Tsuntsaye Ta Bulla a Maradi – 1’46”