Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ana fargabar samun barkewar cutar Marburg a ranar Laraba a wani yankin karkara da ke arewacin Tanzania lamarin da ya kai ga mutuwar mutum takwas.
“Muna da masaniya game da mutane 9 da suka kamu zuwa yanzu, ciki har da 8 da suka mutu,” Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce a wata sanarwa.
“Muna fargabar samun karin mutane da suka kamu a kwanaki masu zuwa yayin da aka inganta tsarin sa-ido kan cutar.” Ghebreyesus ya kara da cewa.
Kamar cutar Ebola, cutar Marburg tana yaduwa daga jemagu masu cin 'ya'yan itatuwa kuma tana yaduwa tsakanin mutane ta hanyar kusanci da ruwan jikin wadanda suka kamu ko kuma abubuwan da suka taba su, kamar zanin gado da sauransu.
Idan ba a tare ta da magani ba, cutar Marburg na iya zama ajali ga har zuwa kashi 88 cikin 100 na mutanen da suka kamu da ita.
Alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon jiki, amai da gudawa, wadanda a wasu lokuta kan kai ga mutuwa.
Babu wani rigakafi ko magani da aka amince da shi a matsayin maganin cutar a yanzu.