Hukumomin kiwon lafiya a jihar Adamawan sun tabbatar da bular anobar cutar kwalaran a kananan hukumomi biyu dake makwabtaka da juna, karamar hukumar Mubi ta arewa da kuma Mubi ta kudu, wanda kawo yanzu aka bayyana cewa mutane 12 sun mutu, yayin da ake jinyar wasu 134 sakamakon kamuwa da cutar.
Tun farko da yake tabbatar da bullar anobar cutar Dr Bwalki Barem Dilli, shugaban cibiyar yaki da bullar cututtuka ta gaggawa ta jihar, wato Emergency Operations Centre,EOC, ya ce tuni aka tura manyan jami’an kiwon lafiya tare da hadin gwuiwar jami’an hukumar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya-WHO, don shawo kan lamarin.
Yace sun soma samun rahoton bullar cutar kwalaran ne daga babban asibitin garin Mubi,inda aka kawo wasu majinyata dake amai da gudawa.
Kuma tuni mutane 12 suka mutu,yayin da ake jinyar 134. Tuni aka debi samfurin kwayar cutar don bincike a asibitin koyarwa na Maiduguri don daukan matakan da suka dace.
Shi dai wannan lamari na faruwa ne a yayinda ma’aikatan jinya a Najeriya ke cigaba da yajin aikin da suke yi, kuma tunihukumomin kiwon lafiya a jihar suka soma gangamin fadakarwa ga al’umma na yadda ake kulawa da tsaftar muhalli don gudun yaduwar cutar, kamar yadda Dokta Dilli ya bayyana. Ya kara da cewa a guji amai da gudawan wadanda suka kamu da cutar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5