An fara zaman makoki na kwanaki biyu a kasar Cuba a jiya Asabar, bayan da wani jirgin saman kasar ya fadi a ranar Juma’a ya kashe mutane 107, ciki har da wasu fasinjoji daga kasar Argentina da Mexico.
Yanzu haka ana kulawa da wasu mutane uku da suka tsira daga hadarin, wadanda bayanai ke cewa suna cikin mawuyacin hali.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ya ruwaito cewa an tsinci daya daga cikin bakaken akwatunan nan masu nadar bayanai, wanda zai taimaka wajen gano ainihin abinda ya haddasa hadarin.
Wani da ya shaida hadarin, ya fadawa Kamfanin Dillancin labarai na Associated Press cewa, jirgin mai shekaru 37 kirar Boing 737, ya yi wani irin diban iska, jim kadan bayan da ya tashi, kafin daga baya kuma ya kama da wuta.
Kamfanin na Boing da ya kera jirgin ya ce yana da wata tawagar kwararru da za ta iya taimakawa wajen bincike, idan ana bukatarsu, amma idan hukumomin Amurka da Cuba sun amince.
Bayanai sun ce kasar ta Mexico ma za ta tura da wasu kwararru biyu.
Shi dai jirgin yana kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Holguin da ke gabashin kasar ta Cuba.