Sama da mutane 100 suka mutu a wani hadarin jirgin saman kasar Cuba, jim kadan bayan da ya tashi daga babban filin tashin jirage da ke Havana.
Jami’ai sun ce mutum uku sun tsira daga hadarin, amma kuma suna cikin mawuyacin hali a asibiti.
Kafofin yada labaran kasar ta Cuba, sun ruwaito cewa jirgin, wanda na gwamnatin kasar ne, na shirin barin filin tashin jirage na Jose Marti ne, a lokacin da hadarin ya auku.
Yana kuma hanyarsa ta zuwa birnin Holguin ne da ke gabashin kasar ta Cuba.
Wani da ya shaida lamarin ya ce, jirgin kirar Boing 737, wanda ya tsufa, ya yi gaggawar dawowa filin tashin jiragen, gabanin ya fadi a wata gonar rogo, jim kadan bayan da ya tashi.
Shugaban kasar ta Cuba, Miguel Diaz-Canel, wanda ya yi hanzarta zuwa inda jirgin ya fadi, ya ce an kashe wutar da ta kama a jirgin, sannan ana kan kokarin gane fasinjojin da ke cikinsa tare da gudanar da bincike kan abinda ya haddasa hadarin.
Hukumomi sun ce akalla fasijoji 104 ne a cikin jirgin da kuma matuka da masu kula da jirgin su shida wadanda duk ‘yan kasar Mexico ne.
Gwamnatin Mexico ta ce an kera jirgin ne a shekarar 1979, kuma wani kamfanin kasar mai zaman kansa ne ya ba da hayar shi ga kasar ta Cuba.
Facebook Forum