A wani zama na musamman da majalisar kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta yi a ranar juma’a, domin tattaun kara lalacewar halin da ake ciki a yankunan da falasdinawa suke, Zeid Ra’ad al-Hussein ya ce daga rayuwarsu har mutuwarsu, mutane miliyan 1 da dubu casa’in a Gaza suna zaune ne a cikin mawuyacin halin a wasu unguwanni masu fama da masifar gubar talauci.
Zaman na musamman zai iya janyo a kafa wata hukumar bincike akan tashin hankalin da ke faruwa akan iyakar Gaza a wannan satin, wanda mutane 60 suka mutu sannan 2,700 suka raunata. A cikin wadanda suka mutu akwai mata da kananan yara wanda suka hada da yarinya yar wata 8.
Jakadan Isra’ila a cikin Hukumar kare hakkin bil adaman ta majalisar dinkin duniya yace binciken tashin hankalin Gazan ba zai canza abubuwan da ke faruwa ba ko kadan.
Tashin hankalin dai ya samo asali ne a sanadin ofishin jakadancin Amurka da aka yi ne a birnin Kudus.
Facebook Forum