Dan wasan gaba na Black Stars, Jordan Ayew ya yaba wasan da kungiyarsa ta Crystal Palace ta yi a wannan sabuwar shekara, inda ta lallasa Sheffield United a wasan Firimiya Lig.
WASHINGTON, DC.. —
Palace ta yi nasara da ci biyu da nema a ranar Asabar a filin wasa na Selhurst, wadanda suka zura kwallayen sun hada da Jeffery Schlupp na Ghana da Eberechi Eze.
Eberechi Eze, da ya maye gurbin shi ne ya ci wani kwallon da ya kai Palace ga samun nasarar farko a shekarar 2021.
Ayew da ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci ya taka leda sosai.
“Mun samu sakamako mai dadi kana mun fara shekarar da murna na maki uku”, inji Ayewa, a wani sakonsa na shafin Instagram.
Karin bayani akan: Crystal Palace, Jordan Ayew, Black Stars, da Premier League.