Dan wasan Palace Wilfred Zaha ne ya zura kwallaye biyu da suka kifar da tsohuwar kungiyarsa ta United, a wasanta na farko na gasar ta Premier ta bana.
Andros Townsend ne ya fara zurawa Palace kwallonta na farko a minti na 7 da soma wasan, kafin bugun fanariti mai cike da cece-kuce a minti na 74 da Palace din ta samu.
Alkalin wasan ya bi shawarar mataimakinsa mai kula da hoton bidiyo akan tabbatar da bugun fanariti din, to amma kuma ya kama mai tsaron gida na United David Dagea da laifin fitowa kafin buga kwallon da ya tare, wanda hakan ya sa aka sake buga fanaritin inda Zaha ya sami jefa kwallonsa ta farko.
Zaha ya kuma jefa kwallonsa ta 2 a minti na 85 na wasan, wanda ya ba da adadin kwallaye 3 da Palace din ta zura, a yayin da sabon cefanen United din Donny van de Beek da ya shigo a matsayin canji, ya zura mata kwallo daya tilo a minti na 80 na wasan.
Wannan ne karon farko a cikin shekaru 6 da United ta sha kashi a wasan ta na farko na bude gasar Premier.
A sauran wasannin da aka fafata na gasar ta Premier a yau, Everton ta lallasa sabuwar shigowa, West Brom da ci 5-2, a yayin daya kungiyar sabuwar shigowa – Leeds United ko ta doke Fulham da ci 4-3.
Facebook Forum