WASHINGTON, DC —
A wasan da kungiyarsa Real Madrid ta yi da Osasuna, Cristiano Ronaldo ya jefa wasu kwallaye biyu masu girgiza zuciya, ya nunawa duniya cewa shi fa ba kanwar lasa ba ce, kuma babu kamarsa.
Wannan nasara, ta kuma ba Real Madrid kuzarin ci gaba da hankoron kambun La Liga.
A bayan da ya ayyana cewa yana jin jikinsa garau kafin wasan na asabar, Ronaldo ya tabgarawa da duniya hakan a filin wasa, inda ya jefa kwallaye biyu, ya kuma rika lailaya ma 'yan wasan Osasuna, kamar dai shi ne zakaran zakaru na tamaula.
Minti 6 tak da fara wasa, ya narka kwallon da golan Osasuna, Andres Fernandez, ba ya da ikon tsarewa tun daga nesa.
Ana komowa daga hutun rabiun lokaci, Ronaldo ya jefa kwallonsa na biyu, wanda kuma shi ne na 30 da ya jefa a wasannin lig-lig na bana.
Daga bisani, an cire Ronaldo domin ya huta. dalili kuwa shi ne akwai karon battar da zata fi janye hankalinsa, watau gwabzawar da zasu yi da kungiyar Bayern Munich ranar talata a karawa ta biyu ta wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai.