COVID-19: Buhari Da Tawagarsa Sun Kebe Kansu Bayan Dawowa Daga London

Shugaba Buhari a lokacin da ya dawo daga London (Facebook/Fadar shugaban kasa)

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari da tawagar da ta raka shi London sun kebe kansa bayan da suka dawo a ranar Juma'a, a wani mataki na bin ka’idar da aka shimfida ga wadanda suka je kasashen ketare don a kaucewa yiwuwar yada cutar COVID-19.

Buhari ya je birnin na London ne don halartar taron koli na bunkasa harkar ilimi a duniya.

Kakakin Buhari Malam Garba Shehu ne ya fadawa gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi inda ya ce shugaban da tawagarsa sun dauki matakin ne saboda bin ka’idar da hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC ta shimfida ga duk wanda ya yi tafiya zuwa kasashen ketare.

Hukumar ta NCDC ta bukaci duk wanda ya yi tafiya zuwa kasashen ketara da ya kebe kansa na dan wani lokacin kafin ya fara cudanya da jama’a don a kaucewa yiwuwar yada cutar COVID-19.

Bayan kammala taron, shugaban Najeriyar wanda ya tafi kasar ta Birtaniya a ranar 26 ga watan Yuli ya kuma tsaya ya ga likitocinsa don su duba lafiyarsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya sauka a Najeriya

A ranar Juma’a 13 ga watan Agusta shugaban na Najeriya ya koma Najeriya.

A karshen makon da ya gabata, aka rufe ofishin jakadancin Najeriya da ke London bayan da wasu ma’aikata biyu suka kamu da cutar COVID-19.

Ofishin zai kwashe kwana goma a rufe kamar yadda hukumomin Birtaniya suka gindaya a matsayin sharadi.

Daga cikin jami’an gwamnatin da shugaban ya tafi da su London, akwai Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoferry Onyeama, karamin Ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, Darekto-Janar na hukumar tattara bayanan sirri, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar da kuma mai ba da shawara kan tsaron kasa Manjo-Janar Babagana Munguno mai ritaya.