Kwanaki kadan kafin a fara Azumin watan Ramadan, kasashen musulmai a fadin duniya na shirin fuskantar yanayin azumi ba kamar yadda aka saba ba sakamakon annobar cutar coronavirus, an kafa dokar nesanta jama'a a daidai lokacin da cudanya kusan ke da muhimmanci a bangaren ibada.
Wata mafi tsarki a tsarin kalandar musulunci shine watan Ramadan wanda ake bukatar hadin kan iyali da jama’a, da al'umma tare da bada taimako da kuma yawaita ayyukan ibada.
Amma a yayin da aka rufe masallatai aka kuma kafa dokokin hana sallah cikin jam’i tun daga kasar Senegal har zuwa kudancin nahiyar Asiya, kusan musulmai biliyan 1, da miliyan 800 ne ke shirin tunkarar yanayin Azumin Ramadan da basu taba gani ba a baya.
Kasashen Musulmai a duk fadin duniya sun shiga cikin wani hali na fargaba gabanin zuwan watan, yayin da ake sa ran fara azumi ranar Alhamis.
Musulmai a ko ina sukan bude kofofin gidajensu don makwafta su je cin abincin buda baki a watan Azumi, amma a wannan shekarar da alamu hakan ba zai yuwu ba.