Adadin wadanda ke dauke da cutar coronavirus a fadin duniya baki daya, ya zarta miliyan 2.3, yayin da kasar Amurka ke kan gaba da karuwar cutar, wasu kasashen kuma na ba da sanarwar raguwar adadin.
Jami’ar Johns Hopkins ta fadi cewa Amurka, wacce nan ne cutar ta fi yawa a duk fadin duniya a yanzu, na da adadin mutum dubu 743,000 da suke dauke da cutar, da kuma wadanda suka rasu mutum kusan dubu 43,000.
Kasar China, wadda nan ne cutar ta fara bulla, ta sanar cewa mutum 16 ne sabbin kamuwa.
Kasar Korea ta kudu kuwa ta sanar cewa mutum 8 ne kacal sabbin kamuwa.
Wannan ne karo na farko a cikin watanni da ta samu adadi kalilan.
A wani bangaren, kasashe da dama na soma sassauta matakan hana cudanya da juna da aka gindaya don dakile yaduwar cutar coronavirus.
Facebook Forum