COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka

Cutar Koronavirus a Amurka

A yau Litinin da yamma shugaba Joe Biden zai yi magana a fadar White House, akan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar, daga nan kuma za a yi shiru na ‘yan mintoci sanna kuma za a kunna candle don tunawa da wadansuka mutu.

Cutar Covid-19

“Nan da shekaru masu yawa jama’a zasu yi magana akan annobar a matsayin wani mummunan tarihi a kasar, yadda aka sami mutane da yawa da suka mutu daga cutar mai shafar numfashi,” Bisa ga cewar kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa Anthony Fauci a hirar shi da tashar CNN jiya Lahadi.

Dr. Anthony Fauci

Don tunawa da gaba dayan wadanda suka mutu, jaridar New York Times ta sanya zanen digo guda 500,000 a shafinta na farko, kowanne digo na zaman mutum daya da ya mutu a Amurka sakamakon cutar.