Wata kotu ta umurci shugabannin mulkin sojan Nijar su saki hambararren Shugaba Mamadou Tandja, wanda su ka mar daurin talala.
Kotun tabbatar da adalci ta Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ( ECOWAS ) ta yanke hukunci jiya Litini cewa an take hakkin Mr. Tandja, kuma ta bayar da umurnin a sake shi. Ba ta bayar da karin bayani ba.
Soja sun hambarar da Mr. Tandja a watan Fabrairu, watanni shida bayan da ya matsa lamba aka yi garanbawul wa kundin tsarin mulki don ya kara wa kansa wa'adi da kuma iko. Wadanda su ka yi juyin mulkin sun yi alkawarin gudanar da zabe don mayar da kasar karkashin mulkin farar hula zuwa watan Afrilu mai zuwa.
Satin da ya wuce, masu kada kuri'a a Nijar sun amince da sabon kundin tsarin mulkin da ya soke canje-canjen da Mr. Tandja ya yi ya kuma share fage don gudanar da sabbin zabuka.