Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kama Makamai A Tashar Jiragen Ruwa A Lagos


Mayakan tsageran Niger Delta dauke da makamai
Mayakan tsageran Niger Delta dauke da makamai

Jami'an tsaron Najeriya sun ce a wannan karon an kama makamai tare da motocin soja wadanda aka ce daga Amurka suka fito

Jami’an gwamnatin Najeriya sun ce sun kama wasu makamai da motoci irin na sojoji da aka tura Lagos daga Amurka.

Wani kakakin rundunar sojojin ruwan Najeriya, ya ce an gano daruruwan harsasai, da bindigogi biyu, da rigunan da harsasai ba su huda su a boye cikin wasu motoci da dama da aka rufe da tamfol a cikin Kwantena mai tsawon kafa 40 a tashar jiragen ruwan tsibirin Tin Can dake Lagos.

Har ila yau kwamandan rundunar mayakan ruwa mai kula da yankin yammacin Najeriya, Rear Admiral Emmanuel Ogbor, yace an tsare wasu mutane biyu dangane da shigar da wasu motocin soja guda 8 wadanda aka yi ma fenti irin na kayan rawar dajin soja, su ma a tashar jiragen ruwan ta Tin can Island.

Admiral Ogbor yace mutanen da aka tsare sun yi ikirarin cewa su sojoji ne daga Amurka. Rundunar mayakan ruwan tana binciken ko akwai hannun wasu a cikin wannan lamarin.

A watan da ya shige, dakarun tsaron Najeriya sun kama wata kwantenar cike da gurneti da nakiyoyi a babbar tashar jiragen ruwan Lagos, kuma an ce wadancan makaman sun fito ne daga kasar Iran.

XS
SM
MD
LG