Ranar Jum’a Amurka ta shiga wani mataki, kamar yadda bayanan da jami’ar Johns Hopkin ta fitar bayan matakin da ta shiga a makon da ya gabata na samun yawan mutanen da coronavirus ta kashe a kasar ya wuce 200,000.
Amurka ce tafi kowacce kasa samun yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus, sai wadanda suka biyo baya sun hada da India da Brazil da Russia kuma Colombia, a cewar jami’ar Johns Hopkin.
A Turai samun sabbin kamuwa da coronavirus ya sa gwamnatoci a fadin nahiyar sake kakaba matakai kan mutane da wuraren sana’o’i.
Fara Minsita Dutch Make Rutte ya kira kara samun cutar a kasarsa da cewa abin damuwa ne sosai, yayin da Netherland ta bayar da rahotan ana samun sabbin kamuwa 2,777 a kullum.
Rutte ya ce yana sa ran sanar da sabbin matakai a mako mai zuwa.
Al’ummar kasar jamhuriyar Czech ma zasu fuskanci sabbin matakai a mako mai zuwa, a cewar ministan Lafiya Roman Prymula, said ai bai bayyana takamaimai irin matakan da za a dauka ba.