CONGO: Yau Za'a Fara Ba Da Allurar Rigakafin Cutar Ebola

Tedros Adhanom Ghebreyesus babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wanda ya bayyana lamarin da cutar Ebola ke ciki a Congo

An samu karin mutuwar mutum daya sanadiyar cutar ebola wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a Congo zuwa 35 yayinda a yau za'a fara ba da allurar rigakafi

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Congo ta bada tabbacin mutuwar wani mutun guda wanda tace cutar Ebola ce takashe shi, wannan ya kawo adadin mutunen da aka tabbatar sun mutu sakamakon wannan cutar zuwa 12.

Wannan mutuwar dai ta faru ne a kauyen Iboko dake arewa maso yammacin gundumar Equateur.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta ce haka kuma akwai wasu mutane 4 da ake zaton suna dauke da wannan cutar a gundumar.

Yanzu kasar tana da mutane 35 da aka tabbatar suna dauke da cutar. Yau Litinin din nan cikin yarda Allah, za’a kaddamar da yin alluran rigakafin Ebola a yankunan Bikora da Iboko a lardin Equateur