Daya daga cikin manyan kungiyoyin fararen hula a Najeriya dake yaki da ayyukan cin hanci da rashawa wato CISLAC ta koka game da yadda jami’an hukumar farin kaya ta DSS suka kai mata wani samame a ofishinta da ke babban birnin tarayyar kasar Abuja.
Wannan lamari dai ya sa an fara nuna damuwa game da kokarin matsawa kungiyoyin dake ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a kasar
Wannan lamari dai ya afku ne a ranar Litinin dake zama ranar hutu ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya inda jami’an hukumar DSS suka kai samame ofishin CISLAC cikin manyan motoci ba tare da kai wata takarda ba kafin gudanar da hakan yanayin da ya matukar kada kungiyar sakamakon kyakyawar dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
“A daidai wannan lokaci, ba za mu iya yanke hukuncin cewa ga dalilin da ya sa hakan ta faru ba, amma duk da haka, irin wannan ziyara mara kan-gado tana nuna karara cewa ana take hakkin bil adama da kundin tsarin mulki ya tanada.” CISLAC ta ce cikin wata sanarwa da ta torawa VOA a ranar Laraba dauke da sa hannun shugabanta Auwal Musa Rafsanjani
Masanin shari’a Barista Musa Arife, ya yi bayani kan matakan da ya kamata a dauka ta fuskar doka kafin kai samame ga duk wanda bukatar hakan ta taso a kan sa.
A wani bangare kuwa Barista Buhari Yusuf ya ce jami’an tsaro suna da hurumin su binciki duk inda suke so muddin suna dauke da takardar da ta ba su iznin su yi hakan.
Lawal baba Otu da ke zama tsohon jami’in da ke ba da shawara kan sha’anin tsaro daga jihar Pilato ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin
“Kamata ya yi, a rubuta musu takarda a ce abu kaza da kuke da shi, mene ne hujjarku akai.”
Kawo yanzu dai hukumar ba ta bayyana dalilanta na kai wannan samame ba, kuma kokarin ji ta bakin shugaban hukumar ta DSS, Yusuf Magaji Bichi ya ci tura.
A cewar Rafsanjani tuni kungiyar ta aikawa shugaban hukumar ta DSS wasika.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya:
Your browser doesn’t support HTML5