Cin Zarafin Mata Da ‘Yan Mata Ya Karu a Lokacin Coronavirus- Gillian Triggs

A daidai lokacin da annobar COVID-19 ke lakume rayuka take kuma shafar kasashen duniya, mata da ‘yan mata da suka rasa matsugunnansu na kara fuskantar hadarin cin zarafi da ya shafi jinsi, a cewar hukumar kare hakkin ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

“Akwai bukatar mu maida hankali sosai akan kare ‘yan gudun hijira, da mata da kananan yara ‘yan mata wadanda suka rasa matsugunnansu a wannan lokacin na annoba. Sune suka fi kasancewa cikin hadarin. Bai kamata ba a kyale masu cin zarafi ko kadan kana kuma babu taimakon da ake ba matan da suka tsira daga cin zarafi, a cewar mataimakiyar shugaban hukumar, Gillian Triggs.”

Dokar hana fita da killace jama'a da aka sanya don dakile yaduwar annobar COVID-19 sun janyo tabarbarewar zamantakewa da tattalin arziki saboda takaita zirga-zirga da rufe duk wasu wuraren ayyuka, a cewar Triggs, ta kuma kara da cewa a halin da ake ciki yanzu ta yiwu wasu iyalai su tilasta mata da yara mata shiga harkar fasikanci ko yin auren wuri.”