Cikin kananan yara da suka yi suna, su ne wadanda suka sami karbuwa a kafar YouTube, kuma daya daga cikin su wanda ya yi fice shine wani yaro mai shekaru 6, da haihuwa mai suna Ryan, wanda ake nunwa a kafar YouTube, yana wasa da 'yar tsana da sauran nau'ukan kayan wasan yara, wanda ke daukar hankalin sauran kananan yara a fadin duniya.
Tun yana da shekaru uku da haihuwa iyayen Ryan, suka fara nuna hotunan bidiyonsa a kafar YouTube, yana bude sababbin ‘yar tsana da kuma sababbin kayan wasan yara da aka fitar da su a lokacin, da kuma baiyana yadda yara zasu yi wasa da su.
A yanzu haka Ryan, ya kasance hamshakin mai kudi kamar yadda mujallar Forbes, ta wallafa sunan sa a matsayin daya cikin wadanda suka fi kowa samun kudi daga wannan kafa ta YouTube. An bayyana shi a matsayin na takwas, ya sami kudi dalar Amurka Miliyan $11, tsakanin 1 ga wata yunin shekarar 2016 zuwa 1 ga watan yunin 2017.
Kananan yara na matukar son kallon tasharsa ta YouTube, har ma wasu yaran sun fara kwaikwayarsa.
Bidiyon farko na Ryans bai yi farin jini ba, amma bayan watanni hudu da kafe bidiyon, jama’a suka fara tururuwar kallon sa, inda Ryan yake duba nau’ukan ‘yar tsana har guda dari (100) a lokaci guda.
A cikin watan Janairu, masu kallon shafin Riyan, suka haura Miliyan guda, kawo yanzu yana da sama da mutane Miliyan 10, duk lokacin da wani ko wata ya dangwala bidiyon Riyan, kudi ne iyalinsa ke samun kudin shiga.