Cikin Sa'o'i 24 Aka Harbe Akalla Mutane 34 A Birnin Chicago

Masu zanga zanga a birnin Chicago

Masu zanga zanga a birnin Chicago

Wata tarzoma da ta taso a birnin Chicago akan yunkurin dakile mallakar bindigogi ta yi sanadiyar harbe mutane akalla 34 cikinsu har biyar sun mutu

Ya sandan birnin Chicago nan Amurka, sunce ba za’a fi karfin su ba, bayan tarzomar ba saban ba da aka yi a karshen mako data hadasa harbin akalla mutane talatin da hudu cikin kasa da sa’o’i ashirin da hudu a cikin birnin.

Biyar daga cikin wadanda aka harba sun mutu ciki harda wata budurwa yar shekara goma sha bakwai da haihuwa da aka harba afuska. Wani dan Sanda ya fadawa jaridar Chicago Sun Times cewa, wannan itace tarzoma mafi muni daya taba gani. Ana zaman zullumi kuma kila tarzomar ta kara muni.

Jami’in yan sanda yace yaji mutane suna magana ta wayoyinsu ta hannu, suna shirin kai hare haren ramuwar gaiya, kuma suna kira ga wasu mutane da suma su dauki matakin kai hare haren ramuwar gaiya.

A makon jiya daruruwan masu zanga zanga suka tare wani babban titin birnin Chicago, domin nuna rashin amincewar su da tarzomar da take da alaka da mallakar bindiga inda suka bukaci magajin garin Rahn Emanuel yi murabus.

Har yanzu magajin garin bai ce uffa ba gameda tarzomar ta karshen mako, to amma ya bukaci a dauki karin matakan dakile yawan mallakar bindiga ba ma a birnin Chicago kadai ba, amma a dukkan jihar Illinois.

A bana kurum, an kashe fiye da mutane dari uku a birnin Chicago, fiye da kowane birni a nan Amurka.