Cigaba da shari'ar Bukola Saraki na jan hankalin 'yan jam'iyyun adawa

Dr Bukola Saraki kakain majalisar dattawan Najeriya a kotu inda yake fuskantar shari'a

Cigaba da yin shari'ar Bukola Sarki na jan hankalin 'yan siyasa musamman na bangaren adawa inda ko a taron yaki da cin hanci da rashawa sun nuna kin amincewarsu da yunkurin sake dokar kotun kiyayewa da'ar ma'aikata inda Saraki din yake fuskantar shari'ar

'Yan siyasa musamman na bangaren masu adawa suna nuna kin amincewarsu da yunkurin sake dokar kotun da ke yiwa Dr Bukola Saraki shari'a.

Wasu 'yan siyasar na ganin ba Bukola Saraki kadai yake da irin wannan laifin ba.

Shugaban jam'iyyar Labor Abdulrazak Salami yace shari'ar akan siyasa ce domin an yiwa Bola Tinubu aka yi masa hukumci aka dawo aka ce an yi kuskure, kuskuren ya tsaya ke nan sai kotun ta gyara kanta. Yace amma har yanzu kotun bata gyara kanta ba. Wai shi ma shugaban kotun ana bincikarsa. Yace kamata ya yi a sake dubawa a sake tantancewa ta yadda tsakani da Allah za'a yiwa mutane hukumci.

Shi ma skataren jam'iyyar NCC Inusa Tanko nada ra'ayi kamar na Salami. Yace ba Saraki kadai ba ne ya yi wannan laifin. Yawancin gwamnonin yakamata a bincikesu. Yace amma wannan tafiyar ta siyasa ce. Wai dama an ce Bukola Saraki ya sabawa jam'iyyarsa ko kuma shugaban kasa dalili ke nan ake bincikarsa. Yace Bola Tinubu ma an sameshi da irin wannan laifin amma an sakeshi. Bai kamata a bari irin wannan abu na faruwa ba.

Uwar kungiyar kwadago ta Najeriya tace ta goyon bayan zaman kotun da'ar ma'aikatan kan Saraki. Jami'in kungiyar Kwamred Nuhu Toro yace a Najeriya ne mutum zai saci akuya sai a kamashi a daureshi bama sai an yi masa shari'a ba amma kuma sai a samu gwamnoni da 'yan siyasa da aka tabbatar suna da laifin halin bera sai a dinga juye-juye domin kada a hulumtasu. Duk wanda ya yi laifi doka ta hukumtashi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Cigaba da shari'ar Bukola Saraki na jan hankalin 'yan jam'iyyun adawa - 2' 54"