ABUJA, NIGERIA - Babban daraktan cibiyar samar da zaman lafiya da diflomasiyya da ci gaban al’umma na jami’ar Maiduguri, Abubakar Mua’zu, ya bayyana cewa littattafan biyu na kunshe da binciken masana kan ayyukan ta’addacin mayakan kungiyar Boko Haram a yankin Jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, da rikicin manoma da makiyya har ma da rikice rikicen kabilanci da na addini a Jihohin Filato da Kaduna
Littattafan dai sun mai da hankali ne kan matsalolin tsaro a Najeriya baki daya dama take hakkin bil’adama wanda gidauniyar MacArthur ta kasar Amurka ta ba da gudumawa wajen aikin binciken da wallafawa. A na kuma sa ran wannan yunkuri zai yi matukar taimakawa al’ummar Najeriya.
La’akari da irin gudumowar da kafafen yada labarai mussaman na zamani a yanar gizo ke takawa wajen bayyana bayyanai da suka jibanci tsaro da take hakkin bil adama, an yi kira ga yan’ jaridu da su yi taka tsantsan tare da gudanar da sahihin bincike don guje yada labarin da ka iya tada zaune tsaye, a cewar Kabiru Dakata na cibiyar wayar da kan al’umma akan shugabanci na gari da tabbatar da aldalci CAAJA.
Ana dai fatan sakkonin da aka tattaro cikin litattafan za su isa ga al’ummar Najeriya tare da amfanansu ta hanyoyi daban-daban wajen rage matsalar al'amuran tsaron tare da tauye hakkin bil’ adama a kasar.
Saurari cikakken rahoton daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5