Cibiyar kula da harkokin kasuwanci ta Amurka jiya Litinin, ta bada sanarwar fara bincike kan yadda kamfanin sada zumunta Facebook yake adana bayanan masu hulda da shi.Wannan ya biyo bayan rahotanni da suke nuni da cewa, anyi amfani da bayanan miliyoyin masu hulda da kamfanin ta hanyoyi da basu dace ba, bayan da suka fada hanun wani kamfani mai tantance dabi'u ko halayyar mutane mai cibiya a Ingila da ake kira Cambridge Analytical.
Sanarwar da cibiyar ta bayar ta sa farashin hannayen jarin Facebook sun fadi da kashi biyu, kari kan faduwar darajar hannayen jarinsa da kashi 14 a makon jiya, mataki da ya rage darajar hannayen jarin kamfanin da kamar dala miliyan dubu 90.
Galibi dai cibiyar bata sanar da matakan da take dauka na gudanar da bincike, amma ta gaskanta haka, bayan da rahotanni masu yawa a makon jiya suka sanar da cewa cibiyar ta fara gudanar da bincike kan Facebook.